Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Biya Wa ‘Yan Asalin Jihar Miliyan 57 Domin Yin Karatun Digiri A Jam’iar Istiqama

0 108

Hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Jigawa ta mika wa ’yan asalin jihar Jigawa 31 takardar shaidar samun gurbin karatun digirgir a jami’ar Istiqama dake Sumaila a jihar Kano.
Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Saidu Magaji ne ya gabatar da takardun a yayin wani takaitaccen biki da aka gudanar a hedikwatar hukumar dake Dutse. Ya ce gwamnatin jihar ta biya wa daliban kudin makaranta miliyan hamsin da bakwai da dari biyar da goma sha daya da kudin masauki na tsawon shekaru uku. Alhaji Saidu Magaji ya shawarci daliban da suka yi nasara da su mai da hankali akan karatunsu, su kuma kasance jakadu nagari a jihar.
Wasu daga cikin daliban sun yabawa gwamnati bisa wannan karimcin tare da yin alkawarin tabbatar da amincewar da aka yi musu.
Iyaye da masu kula da daliban sun kuma godewa gwamnatin jihar Jigawa kan daukar nauyin ‘ya’yansu zuwa karatu a jami’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: