Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Sabuwar Matatar Man Dangote Dake Legas

0 66

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar babbar matatar mai da hamshaƙin ɗan kasuwar nan na nahiyar Afirka Aliko Dangote ya gina.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Bashir Ahmad ya wallafa hakan ne a shafinsa na Tuwita inda yace za’a ƙaddamar da katafariyar matatar man da aka fara ginawa tun shekarar 2016 nan da mako biyu masu zuwa.

Kamfanin ya gina matatar ne da a kowacce rana za ta iya tace gangar mai 650,000, da nufin magance shigar da tataccen mai cikin ƙasar, kasancewar kasar ta fi kowacce ƙasa arzikin man fetur a nahiyar Afirka.

A cewar sa shugaba Buhari zai ƙaddamar da matatar da ke Legas a ranar 22 ga watan Mayun da muke ciki, kafin wa’adin saukarsa daga mulki.

Mai magana da yawun kamfanin na Dangote ne ya tabbatar da lokacin ƙaddamar da matatar, to sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

Ana tunanin matatar ta laƙume kudi kimanin dala biliyan 19 fiye da yadda aka yi hasashen za ta laƙume tun farkon fara ginata, sakamakon jinkirin shekaru da aka samu wajen ginata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: