Shugaban Kasar Kenya Ya Aiko Da Jakada Na Musamman Domin Tattaunawa Da Tinubu

0 78

Yayin da ranar 29 ga watan Mayun da muke ciki ke kara karatowa domin bikin rantsar da zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Kenya, Williams Ruto, ya aike da jakada na musamman domin tattaunawa da zababben shugaban kasar Kenya kan batutuwan da suka shafi moriyar juna tsakanin Najeriya da Kenya.

Mista Ruto, a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu da kan sa, ya taya Tinubu murnar nasarar da ya samu a zaben tare da mika wasikar sada zumunci ga shugaban kasar mai jiran gado.

Shugaban na Kenya ya yi tayin yin aiki tare da Tinubu domin karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasarsa da Najeriya.

Wakilin shugaban kasar Kenya, kuma shugaban ma’aikatan gwamnati na kasar Kenya, Felix K. Koskei, shine ya mika wasikar, a lokacin da yake ganawa da zababben shugaban kasar a karshen mako a Legas.

A nasa bangaren Bola Ahmed Tinubu ya bayyana muradinsa na yin aiki tare da shugaban kasar Kenya da sauran shugabannin kasashen Afirka wajen fafutukar kare al’amuran da suka shafi kasashen biyu. Ya yi alkawarin yin aiki tare da kasar Kenya a fannonin bunkasar tattalin arziki, ci gaba da magance matsalar rashin tsaro ga al’ummar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: