Masu Zawarcin Kujerar Kakakin Majalisa Sunyi Allah Wadai Da Wandanda Tinubu Ya Nuna Wa Goyon Bayansa

0 67

Masu neman kujerar kakakin majalisar wakilai a majalisa ta 10 na ci gaba da yin Allah wadai da matakin da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dauki na zaben dan majalisar wakilai Tajudeen Abbas na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Zariya a jihar Kaduna a matsayin wanda yake goyan baya.

Da yake fitowa daga wani taro a karshen mako, Tinubu, ya amince da takarar Abbas da Ben Kalu na jihar Abia a matsayin kakakin majalisa da kuma mataimakinsa.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan zababben shugaban kasar ya ayyana Sanata Godswill Akpabio na jihar Akwa Ibom da Sanata Jibrin I. Barau a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa.

Manyan majiyoyi sun ce shugaban majalisar Femi Gbajabiamila da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai na goyan bayan takarar Tajudeen Abbas. Wasu daga cikin ‘yan takarar dake neman wannan kujerar da suka hadar da mataimakin kakakin majalisar Ahmed Idris Wase daga jihar Plateau da Muktar Betara Aliyu daga jihar Borno da Yusuf Adamu Gagdi daga jihar Plateau dukkaninsu sunyi fatali da zaben Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu kamar yadda Bola Tinubu ke goyan bayan takararsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: