Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kasa Ta Ceto Mutane 58 Daga Hannun Garkuwa Da Su A Jihar Kogi

0 75

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta ce ta ceto mutane 58 da wasu gungun masu aikata laifuka da suka yi garkuwa da su a tsakiyar jihar Kogi.

Ba a dai bayyana tsawon lokacin aka dauka ana tsare da mutanen ba.

Wata mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ta ce aikin hadin gwiwa ya basu nasarar ceto mutanen a dajin Udulu wanda aka gudanar tare da wasu kungiyoyin sa kai na yankin.

Ta ce masu garkuwa da mutane sun tsere da raunuka kuma daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ya mutu a yayin samamen.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da Shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu wanda za’a rantsar a karshen wannan watan ke fuskantar kalubalen tsaro da dama da suka hada da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa. Da kuma matsalar yan fanshin daji wanda zama ruwan dare gama gari a jihohi da dama a mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: