RANAR CUTAR SIKILA TA DUNIYA: Duk shekara ana haifar jarirai 150,000 dake dauke da ciwon a Najeriya

0 124

Cutar sikila ko amosanin jini na daya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS.

Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia, mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki daya.

An ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar yaki da cutar amosanin jini wato sikila a duniya. Rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakar da al’umma kan wannan cutar a matakin kasa da kuma na kasa da kasa.

Najeriya ta fi yawan masu cutar a duniya

Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haifar jarirai 300,000 a duniya kuma rabi daga wannan yawan a Najeriya ake haifar su. Daga cikin 150,000 na Najeriya din nan 100,000 ne ke mutuwa duk shekara.

Alkaluma sun nuna cewa mafi yawan masu cutar suna arewacin kasar ne. Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewar rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu dauke da cutar sikila a kasar.

Masu fama da cutar sikila suna fara shan wasu magunguna tun daga lokacin da aka gano suna dauke da cutar har zuwa karshen rayuwarsu, kamar yadda Dr Bashir Isa Waziri, wani likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano ya shaida mana.

”Daga cikin magungunan akwai ‘Folic Acid’ wanda yake kara musu jini, saboda kwayoyin jininsu na yawan karewa. Akwa kuma ‘Paludrine’ magani ne da ke kare su daga kamuwa da cutar maleriya don tana wahalarsu sosai idan suka kamu.

Sai maganin ‘Peniciillin V’ shi kuma aikinsa shi ne kare su daga cututtuka masu alaka da numfashi. Sai ‘Hydroxyurea’ wanda yake taimaka wa kwayoyin jinin siffarsu ta zama mai kyau, yake kuma taimaka musu wajen rage tashin ciwon. Amma yawanci shi sai wanda ciwon ke masa tsanani,” in ji likitan

Tsananin zafin ciwon kwankwaso da masu cutar kan yi fama da shi lokaci zuwa lokaci yana matukar uzzura musu. Kwararru a harkar lafiya sun ce zafinsa ya fi na nakuda.

Dr Bashir Waziri ya ce: “Suna jin ciwon kashi kamar ana kwankwatsa shi, jini ba ya isa wasu wuraren don haka idan suka taru a waje daya sai su saka ciwo.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: