

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutun ranar demokradiyya ta bana.
Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a madadin gwamnatin tarayya.

Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Georgina Ehuriah, ta jiyo Aregbesola na taya ‘yan Najeriya murnar dorewar mulkin demokradiyya a kasarnan.
- Why price of cement is high? -Dangote
- Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Ya Yiwa Gwamna Badaru Ta’aziyar Rasuwar Dan Uwansa
- Za A Yi Kididdigar Masu Aikin Karuwanci A Bauchi
- Kuji tsoron Allah ko koma gare Shi, Atiku yayi kira ga yan Najeriya.
- Goodluck Jonathan: Kuri’un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da godewa kokarin da aka yi wajen dawo da mulkin demokradiyya.
Ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya jajircewar gwamnatin tarayya wajen yaki da annobar corona tare da hadin kan dukkan ‘yan Najeriya.