

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da cewa marasa lafiya 222 daga cikin 283 da suke fama da cutar corona a jihar an sallame su.
Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya sanar da hakan jiya Litinin lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Dutse.
- Tarihin Gamuwa 10 Tsakanin Kano Pillars VS Eyimba Da Kuma Wasan YauYau za a sake ɓarje gumi a mako na 5 na gasar NPFL amma sai dai kuma dukkansu biyun manyan ƙungiyoyi ne a gasar.
- Abubuwa 5 da suka zama wajibi lokacin sanyiLokacin sanyi a kasar Hausa sau daya yake zagayowa a duk shekara, amma mutane da yawan gaske da zarar ya zo sukan ke gwamma na zafi. Ko menene dalili?
- An ƙaddamar da kudin kariya ga ƴan jarida da masu fafutukar ƴancin amfani da yanar gizoKundin dai an kaddamar da shi ta yanar gizo a jiya wanda ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai da masu kare hakkin dan Adam da sassan nahiyar Afrika.
- Yadda ake duba suna don zama ma’aikacin damara na 2020 a NijeriaAna bukatar duk mai neman aikin ya shigar da bayansa cikin adireshin don sanin wuri da lokacin rubuta jarrabawar tantancewar
- Me Ƙungiyar Izala ta ce kan matsalolin tsaro a Najeriya?Shugaban Kungiyar wa’azin musulunci ta Izalatil Bid’ah, Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, yayi Allah wadai da kisan gilla da kungiyar Boko Haram tayiwa manoman shinkafa ‘yan asalin jihar Sokoto, a kauyen koshobe da ke yankin karamar hukumar Jere a jihar Borno wanda alkaluma suka nuna mutum 46 sun rigamu gidan gaskiya.
Yace an sallami marasa lafiyar saboda sun warke daga cutar corona.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa ta dage dokar kulle data hana cin kasuwa a jihar.
A cewarsa, Almajirai 120 na daga cikin wadanda aka sallama, wanda ya kawo saura Almajirai 2 kacal da basu gama warkewa ba, suka rage a wajen killace mutane.