Yan Tada Kayar Baya Na Cigaba Da Shan Kashinsu A Hannun Sojojin Nijeriya

0 183

Helkwatar tsaro tace sojin sama na opearation Hadarin Daji sun lalata karin wani sansanin barayi tare da kashe batagari da dama a dajin Kwayanbana a jihar Zamfara.

Jagoran yada labaran ayyukan tsaro, John Enenche, cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Abuja yace anyi luguden wuta ranar 7 ga watan Yunin da muke ciki, a cigaba da yakin sama da ake gudanarwa karkashin shirin operation accord.

Majon Janar Enenche yace an samu nasarar bayan wani rahoton sirri, leken asiri da sa’ido ya tabbatar da cewa an boye wasu tantuna a karkashin duhun bishiyoyin dajin.

Yace rahoton sirrin ya kuma bayyana cewa ana amfani da kogo da ake samu a wajen a matsayin maboyar barayin tare da sanannen jagoransu, Dogo Gede.

Leave a Reply

%d bloggers like this: