Kasashen Afirka sun amince su yi magana da murya daya domin yaki da ta’addanci

0 180

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya ce kasashen Afirka sun amince su yi magana da murya daya domin yaki da ta’addanci da kuma dakatar da shigowar makamai a tsakanin kan iyakokin kasashen.

Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da hakan ne bayan babban taron yaki da ta’addanci a Afrika da aka gudanar a Abuja.

Ministan ya ce wakilai daga kasashen Afirka sun yanke shawarar hada kansu wuri guda a matsayin kungiyar tarayyar Afirka da nufin bullo da dabarun hadin gwiwa na kasa da kasa don magance ta’addanci a Afirka.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ce lokaci ya yi da kuma da taimakon Allah wajen cimma manufofin da aka sa gaba.

A wajen taron, ministan ya ce akwai hadin gwiwa domin samun bayanai kan ayyukan ta’addanci da hanyoyin samun kudaden ta’addanci da makaman da ake saye.

Ya ce Najeriya na bukatar hadin kai da tallafawa sauran kasashen Afirka wajen magance ta’addanci a kan iyakokin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: