Rarara Ya Soki Davido Kan Nuna Sunayen Yaran Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Oyo A Wajen Kide-kide A Amurka
Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya soki matakin David Adeleke na sanya riga mai ɗauke da sunayen yaran da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo yayin wani taron kide-kide da ya gudanar a ƙasar Amurka.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa domin mayar da martani kan lamarin, Rarara ya bayyana cewa abin da Davido ya yi bai dace ba, yana mai cewa hakan na iya zama kamar bayyana wasu bayanai da suka shafi matsalolin tsaro na Najeriya a gaban idon duniya.
Rarara ya ce, a maimakon irin wannan salo, ya kamata a nemo hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalar ba tare da jawo abin da ya kira “tozarta martabar ƙasa” a idon ƙasashen waje ba.
Sai dai wasu na ganin matakin da Davido ya ɗauka wata hanya ce ta wayar da kan jama’a da kuma jawo hankalin duniya kan halin da iyalan waɗanda abin ya shafa ke ciki. Lamarin ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon bayan ra’ayin Davido, yayin da wasu kuma ke mara wa Rarara baya.