Sanusi II Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Ake Gudanar da Shari’ar El-Rufai, Ya Yi Zargin Rashin Adalci

0 142

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da shari’ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, inda ya yi zargin cewa akwai yunƙurin hana shi samun beli.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya yi amfani da batun El-Rufai a matsayin misali wajen jaddada muhimmancin tabbatar da adalci da bin doka da oda ba tare da nuna son kai ko wariya ba.

Sanusi II ya ce ya zama wajibi a gudanar da dukkan shari’o’i cikin gaskiya da adalci, tare da mutunta haƙƙin waɗanda ake tuhuma kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa da dokoki suka tanada.

Ya kuma yi zargin cewa wasu alkalai na tafka rashin adalci a wasu shari’o’i, yana mai kira ga hukumomin shari’a da su tabbatar da cewa kowa ya samu damar kare kansa cikin yanayi na gaskiya da adalci.

Leave a Reply