Kungiyyar cigaban masarautar Hadejia (HEDA) ta dora alhakin ambaliyyar ruwan da ke faruwa akan gwamnatocin yanzu da na baya na tarayya da jiha.

Masarautar dake yankin arewa maso gabas na jihar Jigawa, tana da kananan hukumomi 8 a karkashinta, wadanda suka hada da Hadejia, Kaugama, Auyo, Malammadori, Birniwa, Guri, Kirikasamma and Kafin Hausa.

Masarautar Hadejia

Shugaban kungiyyar , Abdullah Sarki Kafinta, wanda ya zanta da manema labarai anan cikin garin Hadejia, ya bayyana takaicin sa kan yadda al’ummar cikin garin Hadejia suka rasa kadarorinsu, gidaje da rayukansu sanadiyyar ambaliyyar ruwan.

Sannan yayi kira ga gwamnatin tarayya da taimakawa al’ummar yankin da irin shuka daban daban da irin kifi daza a zuba a kududdufai idan ambaliyyar ruwan ta wuce.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: