Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa a jiya ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 dasu dakatar da karbar sabon kudin wuta wanda suka fara a ranar 1 ga watan Satumba, na tsawon makonni biyu.

Umarnin dakatarwar dauke da kwanan watan 28 ga watan Satumba, na dauke da sa hannun shugaban hukumar, James Momoh, tare da kwamishinan shari’ah lasisi da bin umarni, Dafe Akpeneye.

Hukumar tace umarnin dakatarwar za tayi aiki daga ranar 28 ga watan Satumba zuwa 11 ga watan Oktoba, lokacin da zata kare.

A ranar 1 ga watan Satumba, hukuma ta amince da sabon kudin wata na bana domin kamfanonin rarraba wutar lantarki 11.

Biyo bayan amincewa da sabon kudin wutar da hukumar ta yi, nan take kamfanonin rarraba wutar lantarki suka kara kudaden wutarsu, wanda kawo yanzu ake karba tsawon makonni hudu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: