Rikice-rikice sake dabaibaye Najeriya suke

0 117

Majalisar Dokokin Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kafa dokar-ta-baci saboda tabarbarewar tsaro a kasar. Wannan ya biyo bayan yadda kasar ke fafatawa a bangarori da dama da suka hada da masu ikrarin jihadi a arewa maso gabas da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a arewa maso yamma da rikici tsakanin manoma da makiyaya a arewa ta tsakiya da kuma ‘yan aware a kudu maso gabas.

Kakakin majalisar wakilan kasar Femi Gbajabiamila ne ya bayyana matsayin ‘yan majalisar bayan kwashe fiye da sa’o’i uku suna ganawa a asirce.

“Ganin halin da al’amuran tsaro suka kasaance a wannan kasa, lokaci ya yi da shugaban kasa zai gaggauta kafa dokar-ta-bacci a fannin tsaro domin a dauki dukkanin matakan da suka dace wajen dawo da zaman lafiya a kasarmu.” In ji Gbajabiamila.

‘Yan majalisar sun nemi shugaba Buhari da ya tabbatar da daukan matakan gaggawa domin kare muradun gwamnati a fadin kasar, musamman ma cibiyoyin samar da wutar lantarkin da ke Shiroro da ka’inji. Hon. Mansur Ali Mashi, cewa ya yi akwai bukatar rufe kasar baki daya domin bai wa jami’an tsaro dama su gudanar da aikinsu.

Haka ma wasu ‘yan Majalisar Dattawan kasar irinsu Sanata Hassan Muhammad, sun fara nuna kosawarsu da halin rashin tsaron da kasar ke ciki, musamman ganin yadda lamarin ke kara kusanto babban birnin tarayyar kasar Abuja. 

Kusan dukkanin yankunan Najeriya shida na fuskantar matsalar tsaro, kama daga aikace-aikacen ‘yan kungiyar Boko haram, rikicin Fulani da manoma, zuwa masu fafutakar neman kafa kasar Biafra da Oduduwa, lamarin da ‘yan majalisar suka ce na bukatar kiran taron masu ruwa da tsaki.

Ko a shekaran jiya, sai da gwamnan jihar Naija ya sanar da cewar, shi kansa babban birnin Najeriyara wato Abuja na cikin harin, ganin yadda a cewarsa tsakanin sansanin ‘yan kungiyar Boko Haram da babban birnin tafiyar sa’a biyu ce kacal.

Leave a Reply

%d bloggers like this: