Adadin mutanen da annobar Covid-19 ta kashe a India ya haura dubu 200 a wannan Larabar, a daidai lokacin da asibitocin kasar suka cika makil da sabbin majinyatar da suka harbu da kwayar cutar, yayin da jama’a ke ci gaba da gararamba a kan titunan birnin New Delhi da zummar neman iskar Oxygen da magani.

Yaduwar cutar da mace-mace na ci gaba da karuwa a India mai yawan al’umma biliyan 1 da dubu 300, sabanin yadda annobar ta yi sanyi a Amurka da wasu kasashen Turai wadanda tuni suka fara komawa harkokinsu na yau da kullum.

Coronavirus ta lakume rayukan mutane miliyan 3 da dubu 100 a sassan duniya, inda  a yanzu India ta zama cibiyar annobar domin ko a wannan  Larabar sai da mutane dubu 360 suka kamu da ita a kasar baya ga sama da dubu 3 da suka mutu duk a yau din.

Saboda karancin wuraren gudanar da jana’iza a birnin New Delhi, aka mayar da wuraren ajiyar motoci makabartun kona gawarwaki, inda kuma ake kamfan itatuwan kona matattun.

A kokarinsa na kwantar wa da India hankali, kamfanin BioNTech da ya yi hadin guiwa da Pfizer wajen samar da rigakafin Astrazaneca, ya ce, rigakafin zai yi wa kasar aiki.

Tuni kasashen duniya suka fara rige-rigen mika kayayyakin agaji ga India domin ceto ta daga wannan bala’in, inda a baya-bayan Rasha ta yi alkwarin bai wa kasar tarin kayayyakin lafiya da suka hada da na’urar taimakawa marasa lafiya numfashi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: