Rikici ya barke a cikin jam’iyyar APC a Jihar Legas

0 98

Ƴan takara da shugabannin jam’iyyar daga sassa daban-daban na ƙananan hukumomi da yankunan ci gaban ƙauyuka sun nuna ƙin amincewa da yadda wasu manyan kusoshin jam’iyyar ke ƙoƙarin kakaba ‘yan takara, suna zargin cewa ana kau da kai daga gaskiya da adalci.

A wasu yankuna kamar Ojokoro da Yaba, an samu zarge-zargen cewa wasu ‘yan takara da suka fi cancanta an cire su, sannan aka ƙarfafa wata manufa ta “ra’ayin gama-gari” don kakaba wasu da aka fi so ba tare da sahalewar kowa ba.

Wannan lamari ya janyo zanga-zanga daga mambobin jam’iyyar, yayin da wasu ke gargaɗi cewa rashin bin ka’idojin dimokuraɗiyya zai iya janyo illar siyasa ga jam’iyyar a zaben 2027 mai zuwa.

Leave a Reply