Rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta kama wani matashi bisa zargin safarar miyagun kwayoyi a yankin ƙaramar hukumar Ringim

0 75

Rundunar yan sandan jihar Jigawa tayi nasarar kama wani matashi mai shekaru 22 a duniya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi a yankin karamar hukumar Ringim.

Kakakin hukumar ASP Lawan Shiisu Adam ne ya tabbatar da kame matashin a wata sanarwa da ya fitar a birnin Dutse.

ASP Shiisu yace wanda ake zarzin mazaunin garin Ringim ne, kuma ankama shi a ranar 16 ga watan decembar da muke ciki, a lokacin da jami’an yan sanda suka kai sumame wani waje da suke zargin ana aikata laifuka.

Sanarwar tace an samu matashin da mallakamar kwalin kwayar Exol guda 91, da katunan diazepam guda 9, sai wani daurin busashshen ganye da ake zargin tabar wiwi ce, da kuma karan sigari guda 3.

Kakakin yace rundunar yansada bazayi kasa a guiwa ba wajen gurfanar da matashi a gaban kotu.

Kazalika hukumar ta kuma kama wasu mutane 11 a wani sumame da suka kaddamar a wata maboyar sirrin bata gari a yankunan kananan hakumomin Maigatari da Kiyawa a tsakanin ranakun 10 zuwa 12 ga wata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: