Rundunar sojin ruwan Najeriya ta tura jiragen ruwan yaki guda 13 da jirage masu saukar ungulu guda 2 da sojoji dubu 1 da 500 zuwa tekun Guinea

0 89

A jiya ne rundunar sojin ruwan Najeriya ta tura jiragen ruwan yaki guda 13 da jirage masu saukar ungulu guda 2 da sojoji dubu 1 da 500 a wani aikin soji na musamman domin yaki da ‘yan fashin ruwa a tekun Guinea.

Babban hafsan sojin ruwa, Awwal Gambo ne ya sanar da tura sojojin a wurin taron kaddamar da wani shiri da aka gudanar a Onne ta jihar Rivers.

Obi Egbuchulam, wanda ya samu wakilcin babban jami’in rundunar sojojin ruwa ta tsakiya, Awwal Gambo ya bayyana cewa akwai sojojin ruwan kasashen waje uku da zasu shiga aikin.

Ya ce aikin na kwanaki shida zai nemi shawo kan yawaitar da hare-haren da barayin man fetur ke kai wa kan muhimman cibiyoyin mai da iskar gas da kuma sauran masu aikata miyagun laifuka a yankunan ruwan Najeriya.

A cewar Gambo, laifukan sun hada da satar fasaha da fashin teku da kamun kifi ba bisa ka’ida ba da kuma hada-hadar man fetur ba bisa ka’ida ba, da safarar mutane, makamai da muggan kwayoyi.

Ya ce aikin zai kara habaka tsare yankin tattalin arzikin kasa da kuma kara horas da sojojin ruwa domin tabbatar da tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: