Rundunar ‘yansanda ta ceto ma’aikatan da aka sace daga jami’ar Abuja da sanyin safiyar Talata

0 113

Rundunar ‘yansanda ta ceto ma’aikatan da aka sace daga jami’ar Abuja da sanyin safiyar Talata.

An bayyana yadda ‘yan bindiga suka kutsa kai cikin jami’ar, suka yi awon gaba da mutane shida, ciki har da farfesoshi biyu.

An samu rahotannin cewa masu garkuwan sun tuntubi iyalan wadanda aka kashe domin neman kudin fansa na naira miliyan 300.

Amma a safiyar yau ne wani jami’in makarantar Dr Abubakar Kari ya sanar da cewa an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da biyan kudin fansa ba.

Hukumar makarantar ta kuma tabbatar da hakan a wani sako da ta wallafa a Facebook.

Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, ita ma ta tabbatar da sakin mutanen amma ba ta yi cikakken bayani ba.

Ta kuma ce an kama wasu da ake zargi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: