Rundunar yan sandan jihar Adamawa sun cafke wasu mutum 14 da ake zargin shahararrun masu garkuwa da mutane ne

0 275

Rundunar Yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da cafke wasu mutane 14 da ake zargin shahararrun masu garkuwa da mutane ne da ke addabar mutanen jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Yola, babban birnin jihar.

DSP Nguroje ya ce anyi kama mutanen tare da wayoyi hannu 19, biyo bayan samun sahihan bayanai daga majiyoyi masu tushe.

Ya ce an damke wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kananan hukumomi uku Nguroje ya ce an kama wadanda ake zargin a kananan hukumomin Fufore, Yola ta Kudu da kuma Jada na jihar.

Ya ce a yayin da ake gudanar da tambayoyi duk wadanda ake zargin sun amsa laifin sace wani Alhaji Sale Idi na Farang a karamar hukumar Fufore da Ya’u Adamu na garin Ganye a karamar hukumar Ganye.

Kazalika, Nguroje ya ce kwamishinan yan Sandan Jihar Aliyu Alhaji ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai dangane da duk wani mutum da ake zargi a unguwarsu ga ‘yan sanda.

Ya kuma ci gaba da ba da umarnin a gudanar da bincike cikin hankali tare da ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda ake zargi da laifi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: