Rundunar yansandan jihar Kano ta kama wani sojan gona wanda yake karɓe kudade a hannun masu Keke Napep

0 112

Rundunar yansandan jihar Kano ta kama wani sojan gona wanda ake zargi da kwarewa wajen karbe kudade a hannun masu keke napep.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai jiya a Kano.

Yace wanda ake zargi da sojan gona sunansa Abubakar Zailani Ibrahim, mai shekaru 27, kuma yana gabatar da kansa a matsayin soja, inda ya kama wani mai keke napep ya kai zuwa ofishin yansanda na Rijiyar Zaki a Kano.

Haruna Kiyawa ya sanar da cewa kwamishinan yansanda Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umarci DPO na Rijiyar Zaki, Usman Abdullahi, ya binciki lamarin.

Haruna Kiyawa yace rundunar zata cigaba kai sumame zuwa maboyar masu aikata laifuka a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: