Sabon ministan da aka naɗa ya sha alwashin tunkarar ƙalubalen da ke tattare da fara aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla
sabon ministan da aka nada, Muazu Sambo, ya sha alwashin tunkarar kalubalen da ke tattare da fara aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla.
Ya yi wannan alwashi ne lokacin da ya bayyana a gaban majalisar dattawa a yau.
Mu’azu Sambo wanda ya fito daga jihar Taraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi minista a ranar Talatar da ta gabata.
Nadin nasa ya zo ne makonni bayan da shugaban kasar ya kori ministocin noma, Sabo Nanono, da na makamashi, Saleh Mamman.
Ko da yake ba a bayyana dalilin da ya sa aka sauke su ba, amma wa’adin nasu musamman na Sale Mamman bai samar da cigaba ko kadan ba a fannin wutar lantarki.
Duk da dai ba a san ko za a nemi Sambo ya jagoranci ma’aikatar wutar lantarkin ba, amma ya tabbatarwa majalisar dattawan cewa ya san al’amuran da ke kawo cikas ga fara aikin tashar wutar lantarkin kuma zai magance su nan da shekara guda.