Mai girma sanatan Jigawa arewa maso gabas sanata Ibrahim Hassan Hadejia ya ziyarci karamar hukumar Birniwa inda ya duba aikin ginin ajijuwa na zamani da ya gina a makarantar Sarkin Arewa Usman Junior Secondary School Birniwa.

Ginin ajijuwan ya banbanta da irin ginin ajijuwa da aka saba. Mai girma sanatan ya fitar da sabon tsari na ginin ajijuwan inda aka samar musu da solar inda take bawa ajijuwan da ofis wuta.

Ajijuwan an kawatasu da fankoki da futulu masu haske wanda zasuna aiki awa ashirin da hudu koda yaushe da wuta cikinsu. Za’a iya amfani da ajijuwan komai dare. An kuma sanyawa ajijuwan fararan alluna wanda za’a iya amfani dasu da projector a koyar da dalibai.

Mai girma sanatan yaje ya duba yadda aikin gini ICT center ta karamar hukumar Kirikasamma yadda aikin yake gudana.

Allah taimaki sanatan al’umma.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: