Sanatan Jigawa ta arewa maso gabas,. Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ya kai ziyara zuwa jamiar Sule Lamido dake Kafin Hausa a shirye shiryen da ake na kafa cibiyar kanikanci da cibiyar fasahar kanikanci ta kasa zata samar.


Mataimakin shugaban jamiar farfesa Sani Lawan Taura ya zagaya da sanatan wurin da ake gina cibiyar.


Cibiyar idan an kammala zata rinka bada takardun shedar digiri da kuma takardar sheda kan kimiyyar aikin kanikanci ga matasa da masu gyaran motoci dake kasar nan baki daya
Idan za a iya tunawa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne ya nemo aikin domin samarda aiyukan yi ga matasa da kuma bunkasa sanaar kanikanci zuwa ta zamani a kasa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: