A daidai lokacin da Najeriya ke sa ran karbar rigakafin AstraZeneca miliyan hudu, Gwamnatin tarayya, da hukumar lafiya ta duniya, da kuma asusun tallafawa kanan yara na majalissar dinkin duniya UNICEF, sun bayyana cewa ma’aikatan lafiya sune na farkon wadanda zasu fara cin gajiyar rigakafin.

A sanarwar da hukumomin suka fitar a jiya, sunce kasar nan ta shirya yiwa a kalla kaso 70 cikin 100 na al’ummar kasar nan rigakafin, daga masu shekaru 18 zuwa sama cikin zagaye na hudu na rigakafin da za’a gudanar cikin shekaru 2.

A gobe talata ne dai kasar na take saran karbar rigakafin kimanin miliyan uku da dubu 92, kamar yadda sakataran gwamnatin tarayya Boss Mustapha Gida ya bayyana. Karbar rigakafin a gobe, shine karo na farko da kasar nan zata samu, kuma kasa ta gaba a yankin Africa da zataci gajiyar rigakafin, bayan kasar Ghana da Cote d’Ivoire.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: