Sanata Mai Mari Elisha Abbo Ya Musanta Zargin Cin Zarafin Wata Mata

0 144

Sanata Elisha Abbo mai wakiltar Adamawa ta Arewa ya musanta zargin cin zarafi da aka yi masa wanda ‘yansanda suka shigar gaban kotu.

An gurfanar da sanatan ne ranar Litinin, a gaban Kotun Majistire, dake Zuba a Abuja.

Mai shari’ah Abdullahi Ilellah, ya bayar da belin sanatan akan kudi Naira Miliyan 5, da kuma mutane 2 da za su tsaya masa.

A kwanakin baya ne dai wani faifan bidiyo ya bazu a kafar sadarwa ta intane dake nuna yadda Sanatan ya zabzabgawa wata mata mari a shagon sayar da kayan batsa, bidiyon da Jaridar Premium Times ta wallafa.

Tun bayan bullar wancan bidiyo ne mutane da dama suka yi ta bayyana ra’ayinsu game da hukuncin da ya kamata a yi masa.

Hakan ta sanya har rundunar yan sanda ta kasa ta gayyace shi domin amsa tambayoyi kafin daga bisa su gurfanar da shi gaban koliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: