Sanata Oluremi Tinubu ta hada hannu da hukumar NPC da UNICEF domin inganta rijistar haihuwa

0 121

Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta hada hannu da hukumar kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin kara inganta rijistar haihuwa a kasar nan tare da kaddamar da shirin, takaddar Haihuwa ta UNICEF/RHI na shekara 2024.

Shugaban NPC, Hon Nasir Isa Kwarra, wanda ya bayyana hakan bayan da ya jagoranci abokan huldar ci gaba ga Uwargidan shugaban Kasar jiya  a Abuja, ya ce taron tunawa da ranar 29 ga watan Agustan 2024 zai nuna babban ci gaba a kokarin gwamnati.

Shi ma da yake nasa jawabin, babban jami’in kula da kananan yara na UNICEF, Ibrahim Sesay wanda ke cikin ziyarar ya bayyana kaddamar da shirin a matsayin muhimmin abu, domin cike gibin da ake samu a fannin rajistar haihuwa da kuma inganta shirin ci gaban da bayanai ke haifarwa ga yara a kasar nan.

Ya jaddada muhimmancin kafa da kuma tabbatar da tsaro na kowane yaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: