Sanatocin uku a Kebbi sun sauya sheka zuwa APC

0 100

Sanatocin uku sun haɗa da Sanata Adamu Aliero da Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi da kuma Sanata Garba Maidoki.

A baya-bayan nan batun sauya sheƙa tsakanin manyan ƴansiyasa na ci gaba da ɗaukar hankali a ƙasar, bayan da wasu jiga-jigan jam’iyun hamayya ke komawa APC mai mulki.

Ko a makonnin baya ma gwamnan jihar Delta da tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa – wanda shi ne ya yi wa PDP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023 – suka sanar da komawa APC.

‘Gaskiya ke halinta’

Sakataren jam’iyyar APC na kasa Malam Bala Ibrahim, ya ce gaskiya ce ke yin halinta.

A wata hira da BBC Malam Bala Ibrahim, ya ce, “Ga masu cewa muna fatan da matsaloli da rigingimu, ai yanzu suna jin kunya, kuma akwai wasu daga cikinsu ma har sun dawo jam’iyyarmu ta APC.”

“Wannan dai na ba wani abu bane face nuni da cewa manufofin jam’iyyar APC manufofi ne na gari wadanda suka zo dai-dai da dimokradiyya. Sanna ga adalci da tsari da ake bukata a dimokradiyya,” in ji shi.

Wasu da suka koma jam’iyyar APC daga jam’iyyun adawar sun ce rikice-rikicen da ake fama da su a jam;iyyarsu ne ya sanya su sauya sheka.

‘Rashin akida’

Sai dai kuma Umar Ibrahim Tsauri, mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya shaida wa BBC cewa rashin akida ce ke sanya wasu sauya sheka.

Ya ce ” Mafi yawan mutanen da ke sauya sheka musamman a yanzu ba mamaki ko dai sun nemi wani abu a jam’iyyar da suke basu samu ba, ko kuma suna hangen cewa a adawa ba a samun komai gara su koma jam’iyya mai mulki.”

Sauya shekar ‘yan siyasa dai abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya.

Masana kimiyyar siyasa a Najeriya dai sun ce ‘yan siyasar kasar basu gaji azumin siyasa ba. Salon sauya shekar dai na tasiri wajen karawa jam’iyya mai mulki karfi.

Leave a Reply