Sarkin Dutse Hamim Sanusi Ya Godewa Shugaba Buhari Bisa Samar Da Sabuwar Bataliyar Soji Ta Yargaba

0 79

Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Hamim Nuhu Muhammad Sanusi ya kai ziyara ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari a fadarsa dake Birnin tarayya Abuja.

Mai martaba Sarki yace ya kai ziyarar ne domin godewa shugaban kasa bisa samarda sabuwar bataliyar soji a garin Yargaba ta karamar Hukumar Dutse.

Ya kuma bukaci Shugaban kasa da ya taimaka wajen samarda makaranta da kuma asibiti a Barikin domin amfanin alummar yan kunan.

Mai Martaba Sarki na Dutse ya kuma roki Shugaba Buhari da ya taimaka wajen ganin an fara katafaran aikin samar da ruwan sha na garin Dutse. A lokacin ziyarar, mai Martaba Sarkin ya samu rakiyar Wazirin Dutse Alhaji Bashir Dalhatu da sauran yan majalisar sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: