Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa jin waƙa yana ƙara nutsuwa, imani, ƙwazo da kuma zaburar da mutane.

Malam Khalil ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a wajen maulidin Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) na gidan Sheikh Malam Nasidi Abubakar Goron Dutse dake unguwar Goron Dutse a cikin birnin Kano.

Sheikh Ibrahim Khalil

Malamin, wanda shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ya ce: “Shi yasa da idan ana aikin gayya a kan kirawo Shafi’u, wani babban mawaƙi na Kano, da shi da masu kaɗa masa ganga, ana kaɗawa ana gangi ana waƙa, a kawo kunu a sha.

Wasu lokuta ma a afa wani abu– ka ji garau, to a lokacin kai bai waye ba a lokacin, sai a dama a cikin kunu su sha, ka gan shi yana ta tsalle, har da to haka ake yi.

“To wannan saboda ɗan Adam, shi yasa za ku ga a cikin Sahihul Bukhari, lokacin da aka zo ana yin Masallacin Annabi (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi), da lokacin da ake haƙa Ramin Gwalalo, to ana rera waƙa, to Annabi ba ya rera waƙa, amma su sahabbai suna rerawa”.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: