Labarai

Shugaba Buhari a ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta rayuwar ‘yan Najeriya duk da mummunan yanayi na zamantakewa da tattalin arziki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin wannan mako ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta rayuwar ‘yan Najeriya duk da mummunan yanayi na zamantakewa da tattalin arziki.

Ya ce kaunarsa da kishinsa na inganta rayuwar ‘yan Najeriya bai gushe ba, yana mai kira ga ‘yan Najeriya da su kara hakuri, juriya da jajircewa.

Shugaban kasar ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tsaffin shugabannin tsohuwar jam’iyyar a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata.

Sai dai ya bukaci shugabannin siyasa da su mai da hankali tare da tabbatar da manufofin inganta muradun kasarnan.

Shugaban kasar ya ce bai kamata a bar san zuciyar da ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane kusan miliyan guda a tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 ya sake maimaituwa ba.

Shugaban kasa, wanda kuma shine Ministan Albarkatun Man Fetur, ya kuma amince da sayen kamfanin mai na Mobil wanda kamfanin makamashi na Seplat na ‘yan Najeriya yayi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: