Shugaba Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron shugabannin kasashe na rainon Ingila wanda za a gudanar a kasar Rwanda

0 79

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron shugabannin kasashe na kungiyar kasashe rainon Ingila wanda za a gudanar a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, nan da mako mai zuwa.

Jakadan Rwanda a Najeriya, Stanislas Kamanzi, shine ya sanar da haka a wajen zaman ganawar shirye-shiryen taron da aka gudanar a Abuja.

Ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amsa gayyatar shugaban kasar Rwanda.

Za a gudanar da taron tsakanin ranakun 20 zuwa 26 ga watan da muke ciki.

Stanislas Kamanzi yace dandalin taron zai kasance wajen tattaunawa da daukar matakai masu muhimmanci da suka shafi rayuwar kowa, wadanda suka kun shi matakan dokoki da dorewar tattalin arziki, yanayi, lafiya, fasaha da kuma matasa.

Jakadiyar Burtaniya a Najeriya, Catriona Laing, tace Birtaniya yanzu a shirye take ta mika ragamar mulkin na kungiyar kasashe rainon Ingila ga kasar Rwanda bayan shekaru hudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: