Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabbin taraktoci na zamani guda dubu 2,000 domin bunƙasa harkokin noma da ƙara samar da abinci a faɗin ƙasar nan.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya ƙaddamar da wannan shiri a ƙarƙashin ajandar samar da isasshen abinci ga al’umma da kuma fitar da kayan gona zuwa ƙasashen waje.
Yayin bikin buɗe sabuwar cibiyar sarrafa irin shuka a Sheda, kan hanyar Abuja zuwa Lokoja, Shugaba Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na zamani da inganta noma ta hanyar na’urori da sabbin dabaru.
Ministan noma, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa baya ga taraktoci dubu 2,000 da aka samo daga ƙasar Belarus, an kuma sayi motocin gyara 12 da kayan gyaran na’urori kusan guda dubu 9,000 domin kula da su a tsawon lokaci.
Gwamnati na shirin amfani da waɗannan taraktoci a kan akalla eka dubu 550,000 na gonaki tare da samar da ayyukan yi ga mutane dubu 16,000 da kuma samar da tan miliyan biyu na kayan abinci. Taron ƙaddamarwar ya samu halartar Mataimakin Firaministan Belarus, Viktor Karenkevich, wanda ya isar da saƙon shugaban ƙasarsu Alexander Lukashenko, yana mai tabbatar da goyon bayansu ga Najeriya na ci gaba da samar da abinci ta hanyar haɗin gwiwa da kuma kimiyya da fasaha.