Shugaban APC na samun caccaka bayan kalamai da ya yi babu matsala idan Najeriya ta koma tsarin jam’iyya ɗaya

0 691

Shugaban jam’iyyar APC na ci gaba da shan suka da caccaka bayan wasu kalamai da ya yi cewa babu matsala idan Najeriya ta koma tsarin jam’iyya ɗaya.

Kalaman da Abdullahi Umar Ganduje, ya yi cewa idan duk jam’iyyun siyasa za su narke su koma APC, suna maraba da hakan, to sai dai ‘yan adawa na cewa kalaman Ganduje tamkar yi wa tsarin dimokraɗiyya karan tsaye ne.

Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce bai yi mamaki da kalaman na Ganduje ba, saboda a cewarsa bai san darajar dimokraɗiyya ba, ballantana wanzuwar jam’iyyun siyasa a tsarin.

Ya ƙara da cewa tsarin da Gandujen ke son Najeriya ta koma, tsari ne da ko a ƙasashen da suka ci gaba irin Amurka da Ingila ba a yinsa.

A baya-bayan nan dai an riƙa samun sauyin shekar jam’iyyar hamayya zuwa APC mai mulki.

Leave a Reply