Lamido ya bukaci Shugaba Tinubu da ya biya iyalan MKO Abiola bashi da yake bin Najeriya na Naira biliyan 45

0 195

Tsohon Sakataren Jam’iyyar SDP kuma tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce gwamnatin soja ta soke zaben Shugaban kasa na 1993 da MKO Abiola ya lashe ne saboda bashi da yake bin Najeriya na Naira biliyan 45 tun zamanin Marigayi Janar Murtala Mohammed.

A cewarsa, sojojin sun tsorata da cewa da ace Abiola ya zama shugaban kasa, da sai ya bukaci a biya shi wannan bashi, wanda hakan ka iya durkusar da tattalin arzikin kasar.

Lamido ya bukaci Shugaba Tinubu da ya biya iyalan Abiola wannan kudi domin rufe shafin rikicin zaben 12 ga Yuni gaba daya.

Ya ce a ziyararsa ga Janar Ibrahim Babangida, ya tabbatar masa da cewa Abiola yana bin wannan kudi, kuma yana da muhimmanci a biya shi don adalci da kammala wannan shafi na tarihi.

Leave a Reply