Majalisar Wakilai ta yi watsi da wani kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman tilasta raba kujerun Shugaban kasa da mataimakinsa tsakanin shiyyoyin siyasa guda shida na kasar nan.
Kudirin ya kasance daya daga cikin guda bakwai da aka gabatar don tattaunawa, amma dukkansu aka ki amincewa da su a zaman ranar Talata karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu.
Yayinda aka ba da shawarar sake duba kowanne kudiri a zaman majalisa na gaba, sai dai wannan kudiri na janyo cece-kuce inda wasu ‘yan majalisa suka ce ya sabawa tsarin mulki, yayin da wasu suka ce zai rage rashin daidaito a kasa.
Wasu kamar su Sada Soli sun ce hakan zai haifar da rikici tsakanin yankuna, yayin da wasu suka goyi bayan sa da cewa zai ba kowane yanki damar shiga mulki, amma suka gargadi yiwuwar samun sabbin matsaloli da rikici.