Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa shi da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, da sun tunkari Shugaba Bola Tinubu game da yadda Najeriya ke tafiya a yanzu da ace har yanzu suna kan kujerun gwamnoni.
Amaechi ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata yayin kaddamar da littafin tarihin rayuwar Lamido mai suna Being True to Myself.
Ya ce a zamaninsu, su na taka rawar gani wajen kalubalantar gwamnati tare da yin kira ga shugabanci mai gaskiya, kuma sun kasance masu jajircewa wajen kawo sauyi. Ya ce da ace su ne gwamnoni a yanzu, da ba za su zura ido su ga abin da ke faruwa ba, saboda a lokacin su, an san su da tsayawa kyam wajen kare muradun al’umma.