Shugaban Buhari ya umarci shugabannin tsaro da su samo dabarun magance kalubalen tsaro a kasarnan

0 83

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaro da su samo dabarun magance kalubalen tsaro a kasarnan, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Shugaban kasar ya fitar da umarnin a yau, yayin zaman ganawa na awanni 3 tare da hafsoshin tsaro da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya jaddada bukatar dake akwai ta magance ‘yan fashin daji, wanda a cewar hafsoshin tsaro, suna zama annoba, inda suke kashe mutane da furta kalamai domin jawo hankalin mutane.

Ministan tsaro, Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya gayawa manema labaran fadar shugaban kasa bayan zaman ganawar cewa gwamnati ta bibiyi yanayin tsaro a kasarnan inda ta yanke shawarar cewa zata iya shawo kan matsalar tsaro a jihar Zamfara da jihoshin Arewa ta Tsakiya.

Shugaban kasa ne ya jagorancin zaman ganawar tsaro wanda hafsoshin tsaro suka samu halarta a zahirance.

Hafsoshin tsaron sun samu jagorancin ministan tsaro, janar Bahir Magashi mai ritaya, da babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor.

Leave a Reply

%d bloggers like this: