Shugaban Buhari yace kasar Saudiyya mai arzikin man fetur tana yiwa Najeriya abin alkhairi sosai

0 82

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau yace kasar Saudiyya mai arzikin man fetur tana yiwa Najeriya abin alkhairi sosai.

Shugaba Buhari ya fadi haka lokacin da yake karbar bakuncin ministan harkokin wajen Saudiyya, yarima Faisal Bin Farhan Al-Saud, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban kasar yace bisa la’akari da yawan al’ummar Najeriya tare da karancin kayayyakin more rayuwa, kasar na bukatar dukkan kudaden shigar da zata iya samu daga man fetur, wanda shine ginshikin tattalin arzikinta.

Shugaba Buhari, cikin wata sanarwa da kakakinsa, Femi Adesina, ya fitar, yace alaka tsakakin kasashen biyu tana da karfi sosai.

Yarima Al-Saud, wanda ya kawo gaisuwar Sarki Salman Bin Abdul’aziz Al-Saud, yace masarautar Saudiyya tana alfahari da dangantakarta da Najeriya.

Yace kasashen biyu suna da damarmaki masu kyau a tattalin arziki da siyasa, ba wai ga shugabanni kadai ba, har ga sauran jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: