Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya daukaka karar da wata kotu ta yanke masa na tsare shi a gidan Yari

0 70

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci Da Rashawa ta Kasa EFCC Mallam Abdulrasheed Bawa, ya ce tuni ya daukaka karar da wata Kotu ta yanke, masa inda take umartar a tsare shi a gidan Yari.

Abdulrasheed Bawa, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Abuja, inda ya kara da cewa zai kwale Doka ta yi aikin ta yadda ya kamata.

Manema Labarai sun rawaito cewa Wata Babbar Kotu ce a Abuja ta bada umarnin tsare Shugaban Hukumar ta EFCC a gidan gyaran Halayya, biyo bayan yadda hukumar ta ki bin umarnin ta.

Alkalin Kotun, Mai Sharia Chizoba Oji, ya umarci Sufeta Janar na yan sanda ya tabbatar da cewa Shugaban Hukumar ta EFCC yana tsare a gidan gyaran halayyar.

Mai Sharia Chizoba, ya bada umarnin ne biyo bayan karar da Air Vice Marshal Adeniyi Ojuawo, mai ritaya ya shigar, inda ya ke kalubalantar gwamnatin tarayya.

Alkalin Kotun, ya zargi Bawa da kin bin umarnin Kotun, wajen dawo da wata Mota kirar Range Rover da kuma Naira Miliyan 40 mallakin Mista Adeniyi, wanda hukumar ta karba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: