Akwatuna 242 wanda suke karkashin kananan hukumomi 10 na jihar Katsina ne suke fuskantar hadari saboda matsalar tsaro – INEC

0 76

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a jiya ta bayyana cewa Akwai Akwatuna 242 wanda suke karkashin kananan hukumomi 10 na Jihar Katsina da suke fuskantar hadari saboda matsalar tsaro.

Shugaban Sashen Lura da Ayyukan Zabe na Hukumar INEC a Jihar Katsina Mallam Husseni Jafar, shine ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki a Katsina.

A cewarsa, kimanin mutane dubu 142 da 261 ne zasu yi zabe a a wuraren da Akwatunan suke cikin kananan hukumomi 10 na Jihar Katsina wanda suke cikin Barazana.

Mallam Jaafar, ya ce hukumar ta umarci Jami’anta na kananan hukumomin su yi aiki tare da hukumomin tsaro, da Shugabannin Gargajiya da na Addinai domin samar da yanayin da mutanen yankunan zasu yi zabe.

Haka kuma ya ce hukumar ta kafa wani Kwamati wanda zai duba yadda yanayin tsaro ya ke a yankunan domin bawa Akwatunan damar yin zabe a shekarar 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: