Gwamnatin Tarayya ta amince a mayar da hanyar Kwanar-Danja-Hadejia zuwa hannu biyu tare

0 114

Gwamnatin Tarayya ta amince a mayar da hanyar Kwanar-Danja-Hadejia Road, hannu biyu tare da gyara hanyar domin Matafiya a Jihohin Kano da Jigawa.

Ministan Ma’aikatar Ayyukan da Gidaje Mista Babatunde Raji Fashola (SAN), shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce aikin hanyar zai fara daga Shatale-talen Yankaba ta cikin gari zuwa Kwanar-Danja wanda zata taho zuwa Hadejia.

Cikin wata sanarwa da Maitaimakawa Ministan Mista Hakeem Bello, ya fitar ya bayyana cewa kimanin Naira Biliyan 94 da Miliyan 14 ne aikin zai Lakume.

Fashola, ya ce idan an kammala aikin, hanyar zata bunkasa sufuri da zirga-zirga da kuma safarar kayayyaki daga cikin birnin Kano zuwa sassa daban-daban na kasar nan.

Haka kuma ya ce tattalin arzikin mutanen da aikin zai shafa zai sake bunkasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: