Kudurori na 12 masu kyau ne ga jihar Jigawa – Umar Namadi

0 96

Dan Takarar Gwamnan Jihar Jigawa na Jam’iyar APC Mallam Umar Namadi Danmodi, ya gabatar da kudurorin sa 12 wanda ya kuduri aniyar yi, idan aka zabe shi Gwamnan Jigawa ga Malaman Makarantun Gaba da Sikandire 300 domin su amince da su.

Da yake gabatar da Daftarin Kudurorin nasa, a dakin Taro na Ahmadu Bello a Dutse, Danmodi wanda shine Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, ya sha Alwashin kammala ayyukan da Gwamna Badaru Abubakar ya fara da kuma Dorawa akan Nasarorin da ya samu.

Daga cikin abubuwan da zai bawa Muhimmanci sun hada da Ilimi, Lafiya, Ruwan Sha, Fasahar Sadarwa, Noma, da kuma Kyautata Walwalar Al’umma da sauran su.

Dan Takarar Gwamnan na APC a Jigawa, ya kuma sha Alwashin fadada aikin Gona a Jihar nan domin bunkasa tattalin arziki.

Haka kuma ya ce bazai yi watsi da fannin Ilimin Boko da na Addini ba, a matakan Firamare da Sikandire da kuma gaba da Sikandire.

Kazalika, ya sake Jaddada kudurin sa na kare Muhalli, ta hanyar kirkirar Shirye-shiryen hana saran Daji da Shuka bishiyoyi da kuma bunkasa fannin Albarkatun kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: