Ma’aikatan majalisar dokokin jihar Taraba sun fara yajin aiki kan rashin biyan alawus-alawus da gwamnatin jihar ke yi

0 63

Ma’aikatan majalisar dokokin jihar Taraba a karkashin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin ta kasa (PASAN) sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani kan rashin biyan alawus-alawus da gwamnatin jihar ke yi.

Kungiyar ta PASAN ta fitar da sanarwar yajin aikin ne a yau Litinin cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na jiha Ibrahim Bala Yusuf tare da Sakatarenta Abdullahi Abubakar.

Sun bayyana alhinin su na cewa, sunyi yunƙurin zaman tattaunawa da gwamnan jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Darius Dickson Ishaku, amma yaki amincewa ya zauna da su.

Tare da bayyana cewa ba zasu bari wani ma’aikaci ya shiga harabar majalisar dokokin jihar ba.

Suka kara da cewa bazasu dakatar da yajin aikin da sukeyi ba, har sai an biya musu bukatunsu.

Kafin hakan dai SawabaFm rawaito cewa kafin fara yajin aikin kungiyar ta bayar da wa’adin kwanaki 21 domin duba lamarinsu amma gwamnatin jihar tayi watsi da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: