Mutum 20 sun mutu bayan wani hari da wasu yan bindiga suka kai jihar Benue

0 76

Akalla mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wani hari da wasu Yan bindiga suka kai a Ukohol da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue.

Mai baiwa gwamnan jihar Binuwai shawara kan harkokin yada labarai Terver Akase, wanda ya tabbatar da hakan jiya ga manema labarai.

Ya ce Yara da jami’an tsaro na cikin wadanda aka kashe a harin wanda ya faru a ranakun Alhamis da Juma’a.

Harin ya kuma yi sanadiyyar raunata mutane da dama yayin da daruruwan suka rasa matsugunan su.

Harin na baya-bayan nan dai na zuwa ne bayan makonni biyu da aukuwar irin wadannan hare-haren a Gbeji da ke karamar hukumar Ukum dake jihar.

A ranar 19 ga watan Oktoba wasu Yan bindiga suka kai hari Gbeji inda suka kashe mutane 36 ciki har da Yan sanda biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: