Najeriya ta cancanci kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya – Ibrahim Gambari

0 75

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari, ya ce kasarnan ta cancanci kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

A cewarsa, duba da yanda ake tunanin cewa kasar nan, zata zama kasa ta 3 mafi yawan jama’a a duniya bayan kasasahen Indiya da China nan da shekara ta 2050.

Ya kara da cewa, kamata yayi kasar ta zama mai kujerer din-din a majalissar dinkin duniyar.

Yanzu haka dai Najeriya ta dade tana neman zama mamba a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 2017, wakilin Nigeria a Majalisar Dinkin Duniya Tijjani Bande, ya bayyana kwamitin tsaro a matsayin tsohon batu, wanda bashi da tsarin demokradiyya, tare da neman a bawa kasar nan kujerar din-sin.

Ya roki Majalisar Dinkin Duniya da ta nuna kyakykyawan misali wajen amincewa da wannan bukatar.

Shima anasa bagaren Wakilin dindindin na Najeriya a kungiyar ECOWAS Babatunde Nurudeen, ya kuma bukaci a sake fasalin da kuma fadada kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: