Shugaban Karamar Hukumar Gumel Ya Kaddamar Da Aikin Feshin Maganin Sauro A Karamar Hukumar

0 93

Shugaban karamar Hukumar Gumel Alhaji Ahmed Rufai ya kaddamar da aikin feshin maganin sauro a Karamar Hukumar.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Haladu Musa Mele yace hakan zai rage yaduwar kwayoyin zazzabin cizon sauro a yankin.

Yace sun dauki ma,aikatan wucin gadi 25 domin gudanar da aikin feshin na kwanaki biyar.

Alhaji Ahmed Rufai ya shawarci al,umma dasu rinka kula da tsaftar mahalli domin gudun kamuwa da cutuka

A nasa jawabin sakataren KH Magaji Saidu ya yi kira ga magidanta dasu rufe abinci da ruwansha a lokacin feshin maganin sauron Ya kuma shawarci ma,aikatan feshin dasu kiyaye da kaidoji da kuma dokokin aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: