Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ambaci sunan Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar dakile cin hanci da rashawa, EFCC.

A saboda haka ya nemi majalisar dattawa ta amince da nadin da aka yiwa Abdurasheed Bawa.

Mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai da huldar jama’a, Femi Adesina, ya sanar da haka cikin wata sanarwa a yau.

Sanarwar tace Abdurrasheed Bawa, mai shekaru 40 a duniya, ya samu horo a matsayin mai bincike a hukumar ta EFCC, kuma kwararre ne wajen bincike da gabatar da kara kan lamuran da suka shafi damfara da rashawa da satar kudi ta banki da sama da fadin kudade, da sauran laifukan tattalin arziki.

Sanarwar ta kara da cewa Abdurrasheed Bawa yana da digiri na farko akan tsimi da tanadi, da digiri na biyu akan hulda tsakanin kasashen duniya da harkokin diplomasiyya. Sanarwar bata ce uffan ba dangane da makomar Ibrahim Magu, wanda aka dakatar a matsayin mukaddashin shugaban hukumar a bara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: