Shugaban Kasar Brazil zai sanya wata doka wadda zata bawa gwamnati damar takaita ayyukan sabbin kafofin sadarwa

0 87

Shugaban Kasar Brazil Jair Bolsonaro a jiya ya mika wata doka wanda yake so ta bawa gwamnati damar cire tare da takaita ayyukan sabbin kafofin sadarwa, abinda masu sukan gwamnatin sa suka ki amincewa dashi.

Ma’aikatar Sadarwa ta kasar ta ce dokar zata fara aiki nan take da zarar an amince da ita, sai dai har yanzu ana cigaba da nazartar ta.

Sanarwar ta ce dokar zata shafi cire bayanan da ake yadawa da kuma cire shafin ma gaba daya.

Shugaba Bolsonaro, wanda shima an taba cire sakon sa, biyo bayan yada bayanan karya akan cutar Corona, ya ce sabuwar dokar zata takaita yada karerayi a shafikan sada zumunta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: